Kariya daga Bauta da kuma Aikin Dole, Ghana
Kundin Tsarin Mulkin Ghana
Hoto: Office Holidays
Gabatarwa
Matashiya:
Dukkan abin da za a karanta daga wannan gaɓa zuwa ƙarshen wannan shafi, fassara ce kai tsaye daga Kundin Tsarin Mulkin Ghana na shekarar 1996 wanda aka ɗauke a shekarar 2021 daga shafin: https://constitutionnet.org
Sahe na 16: Kariya daga Bauta da kuma Aikin Dole
- Babu wani mutumin da za a riƙe da bauta ko aikatau.
- Babu wani mutum da za a buƙaci ya yi aiki bisa tursasawa.
- Bisa manufar wannan sashe, “Aikin tursasawa” bai haɗa da:
- Dukkan wani aiki da aka buƙata sakamakon yanke hukunci ko umarnin kotu ba; ko
- Dukkan wani aiki da aka buƙaci wani horarren mai aikin ɗamara ko hidimtawa a matsayin aikinsa ko, a yanayin da mutumin da yake da ƙorafi game da hidimtawa a matsayinsa na ɗaya daga cikin Rundunar Askarawan Ghana, dukkan aikin da aka buƙaci wannan mutum a bisa doka ya aikata a madadin waccar hidimtawar; ko
- Dukkan aikin da aka buƙata a kodawane lokaci da Ghana ke cikin halin yaƙi ko a yanayin gaugawa ko wata annoba da ke barazana ga rayuwa da zaman lafiyar al’umma, har ta kai ga cewa buƙatar wannan aiki a bayyane take ƙarara a wannan halin da kowanne irin yanayi da zai iya afkuwa ko yake afkuwa a wannan lokacin bisa dalilan magance wannan yanayin ne; ko
- Dukkan wani aiki a hankalce, da aka buƙata a matsayin ɓangare na ayyukan da aka saba ko wasu wajibobin ‘yanƙasanci.